Majalisar dokokin Jihar Benue ta bai’wa gwamnan Jihar wa’adin kwanaki uku akan ya gaggauta nada hadimi a bangaren tsaro a Jihar.

 

Majalisar ta bai’wa gwamnan wa’adin ne bayan fashin wasu bankuna da aka yi a Jihar a ranar Juma’a.

 

Majalisar ta bayyana cewa fashin da aka yiwa bankunan nada alaka da rashin tuntubar jami’an tsaro, inda kuma aka shafe awanni biyu ana yiwa bankunan fashin.

 

Bayar da wa’adin na zuwa ne bayan kudirin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Otukpo/Akpa, Angbo Kennedy ya gabatar a gaban majalisar.

 

Bayan gabatar da kudirin da dan majalisar yayi, Kakakin majalisar ya tabbatar da kudirin tare da bai’wa gwamnan wa’adin kwanaki uku da ya nada hadiminsa a bangaren tsaro a Jihar.

 

Daya daga cikin mambobin majalisar Godwin Edoh ya bayyana cewa a ya tsallake rijiya da baya, a yayin fashin da aka yiwa bankunan na Otukpo.

 

Edoh ya ce ‘yan fashin sun yi amfani ne da abin fashewa yayin fashin.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: