[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu nan bada dadewa ba zai gabatar da kundin kasafin kudi a gaban zauren majalisar dattawan Kasar.

Shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawan Solomon Adeola ya bayyana hakan ga manema labarai a yayin rantsar da kwamitinsu a ranar Laraba.

Dan majalisar wanda ya fito daga Jihar Ogun ta yamma, ya tabbatar da cewa a makon gobe shugaban zai gabatarwa da masalisar kasafin.
Solomon ya bayyana cewa za su tsaya tsayin daka wajen ganin an tabbatar da kasafin ya biya bukatar al’umma.
Adeola ya bayyana cewa gwamnatin za tayi kokarin ganin kasafi na aiki daga watan Junairun sabuwar shekara zuwa Disamban shekarar ta 2024 mai kamawa.
Kazalika ya ce bayan shugaban ya gabatar musu da kasafin, za su yi duba sosai akan takardun domin fara aiki akansu.
Daga karshe ya bayyana cewa za su sanya idanu akan yadda za a kashe naira Tiriliyan 26 bayan gabatar da kasafin.