Masu garkuwar da suka yi garkuwa da Malamar jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi Dakta Comfort Adokwe sun saketa bayan yin garkuwa da ita a gidan ta da ke unguwar Jaba a garin na Keffi.

 

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa an saki Malamar ne bayan da iyalanta suka biya kuɗin fansa Naira miliyan Biyar.

 

Daya daga cikin yan uwanta ta tabbatarwa da jaridar Punch sakin malamar a ranar Laraba, bayan shafe kwanaki Biyar a hannunsu.

 

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga gidan Malamar ne, inda suka yi harbe-harben iska kafin daga bisani su ka yi awon gaba da ita.

 

Ta ce bayan sakin ta an mikata zuwa Asibiti domin domin kula da lafiyar ta.

 

Bayan yin garkuwa da ita ‘yan uwan Malamar sun dakatar da jami’an tsaro akan yunkurin kubtar da ita, bayan yin gargadi da ‘yan bindigar suka yi kan cewa za su hallaka ta matukar aka yi wani abu akan yunkurin kubtar da ita.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: