Gwamnan Jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa, an samu ci gaba matuƙa a ɓangaren tsaro a jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ƴan jaridu a yau Juma’a, biyo bayan ganawarsa da shugaba Tinubu a fadar shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Gwamnan ya ce “magana ta gaskiya yanayin tsaro a jihar Borno ya ƙaru da kusan kashi 85 cikin 100. Da kuma sauran harkokin bunƙasar tattalin arziki.”

Zulum kuma ya tabbatar da cewa cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar ta Borno, babu wacce take ƙarƙashin ikon ƴan ta’addah yanzu.

Gwamnan ya ƙara da cewa rundunar soji, ƴan sanda, sojojin sama da sauran hukumomin tsaro, suna basu gudunmawa da haɗin kai matuƙar gaske.

Jihar Borno dai ta sha fama da matsalar tsaro a yankin na Gabashin Najeriya fiye da tsawon shekaru goma, daga Ƙungiyoyin Ƴan ta’adda irin su Boko Haram, ISIS da ISWAP.

A Ƙarshe gwamna Zulum ya tabbatar da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar a halin yanzu, yace an samu matukar ci gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: