Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta yi kira ga hukumomin jindadin alhazai na jihohi da su mika kaso mafi mai tsoka na kudaden aikin hajjin jihohinsu domin killace guraben da aka tanadar wa kowace jiha a aikin hajjin wannan shekara ta 2024.

A wani sako da ya aikewa manyan sakatarorin hukumomin jin dadin alhazai, da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki kan shaanin aikin hajji, darakta mai lura da harkokin kudi da ajiya na hukumar, Dr Salihu A. Usman ya ce kiran ya zama wajibi duba da waadin hukumar aikin hajji ta kasar saudiya ta bayar na cewa dukkan mai bukatar yin aikin hajji a bana wajibi ne ya sanya kudaden da aka umarta kafin cikar wa’adin da aka ware nan da watan Disamba mai zuwa.
Dr Salihu ya ce rashin cika umarnin na nuna cewa babu wani sauran shiri na bukatar yin aikin hajjin a wannan shekara.

Ya kara da cewa idan har hukumomin da abin ya shafa suka kasa cika kaidar da aka shimfida, to babu sauran katabus illa a rage adadin jihar da ta gaza tare da mika wani kaso ga jihar da ta shirya kuma take bukata.

Sannan ya roki shugabannin hukumomin jin dadin alhazan na jihohi, da su ci gaba sa kokari tare da bada cikakken hadin kai domin yin aiki tare wanda zai kai ga samun nasara.