Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf,  ya gabatar da kasafin kudi na shekarar

 

2024  a gaban majalisar dokokin jihar, wanda kasafin ya kai naira biliyan 350.

 

A cewar gwamnan za su yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da gaskiya da cika alkawari da rikon amana wajen aiwatar da kasafin kudin  yadda aka tsara.

 

Sannan ya bayyana kasafin kudin a matsayin bani-in-baka ta hanyar gaskiya da adalci, wanda hakan na cikim tsari da kudirin gwamnatinsu na sadaukarwa da saita alamuran da za su kawo cigaba da dorewar arziki a jihar ta Kano.

 

Gwamnan ya ce manyan ayyuka ne za su lashe sama da bilyan 157, yayin da sauran ayyukan za su biyo da kaso daban da aka ware musu.

 

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnan na Kano ya gabatar da kasafin kudi a gaban majalisar, tun bayan darewarsa kan kujerar gwamnan jihar.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: