Kotun sauraron ƙararrakin zaben yan majalisun tarayya da na jihohi a yau Juma’a ta kori ƙararrakin zabe uku da aka shigar gabanta da ke kalubalantar nasarar Sanator Aliyu Wammako,da Abdussamad Dasuki, da Bala Hassan.

Wammako dai dan majalisar dattijai ne da yake wakiltar Arewacin jihar Sokoto a karkashin jam’iyar APC, yayin da Abdussamad Dasuki na jam’iyyar PDP ke wakiltar ke wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a majalisar kasa, sai Hassan wanda yake dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar kudancin da Arewacin Sokoto a majalisar wakilai ta kasa a jam’iyar APC.


A yayin wani hukunci na hadin gwiwa da jagorar alkalan, Justice Josiphine Oyefeso,ta karanto a madadin sauran alkalan, ta ce hukuncin ya tabbatar da nasarar wadanda ake zargi sannan ta kori karar sabida rashin wadatattun hujjoji.
Tun bayan da aka kammala zabe dai a Najeriya, yan takarkaru da jam’iyyu da dama da rashin cin zaben bai yi musu dadi ba, sun garzaya gaban kotunan karbar ƙararrakin zabe domin shigar da kokensu kamar yadda doka ta bada dama.