Majalisar dokokin jihar Kano ta amince wa gwamnan Kano da ya ciyo bashin Naira Biliyan huɗu daga babban Bankin Najeriya CBN. Don ƙarasa aikin tashar wutar lantarki ta Tiga da Challawa.

Amincewar ta biyo bayan goyon bayan ƙudurin da shugaban majalisar Lawan Hussaini mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala a Jami’yyar NNPP yayi a zaman majalisar.

Yayin da yake gabatar da ƙudirin Lawan Hussaini ya ce, bashin ba shi da ruwa sosai, kuma ba shi da wata illa ga tattalin arzikin jihar.

Ya kuma ce idan aka kammala aikin samar da wutar, zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu a jihar.

Aikin samar da wutar dai an fara shi ne tun lokacin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso, inda bayan tafiyarsa gwamnan da ya gabata Abdullahi Umar Ganduje shi ma yazo ya ɗora a zamanin mulkinsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike da takardar neman sahalewar ciyo bashin ga majalisar dokokin wacce kakakin majalisar Ismail Falgore ya karanta a zaman gabanta.

Gwamnan ya ce zasu amfani da kuɗin bashin ne don ƙarasa aikin samar da wutar lantarkin, dan bunƙasa masana’antu, noman rani da kuma haskaka titunan birnin Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: