Kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun Hijirar Falasɗin na majalisar dinkin duniya Philippe Lazzarini ya ce, mutane a Gaza suna ta mutuwa ƙwarai da gaske.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’ar makon da ya gabata.
Ya kuma ƙara da cewa, ba wai suna mutuwa ne kawai saboda hare-haren bama-bamai ba, wasu da yawa zasu mutu ma sakamakon takunkumin turkewa da aka sanya a Zirin Gaza.

“ayyukan da ake buƙata su na samun tasgaro, magunguna su na ƙarewa, abinci da ruwa yana ƙarewa, tituna a Gaza suna cika da ƙazanta, a yanzu da muke maganar nan mutane a Gaza suna ta mutuwa.” Lazzarini ya ce.

Wakilan jaridar Aljazeera ya bayyana cewa, a wani wajen bauta kusa da Masallacin Al-AQSA mutane ƙalilan ne kawai, kuma kamar yadda aka saba a daidai lokacin duk ranar Juma’a wajen cika yake saboda Sallah, amman ranar duk ba a bar su sun shiga ba.
A babbar mashigar Masallacin na Al-AQSA kuwa, sun ga yadda wasu ƴan sandan Isra’ila su ka yi ta cin zarafin mutane, wani mutum har dukansa ɗan sanda yayi saboda yana yi masa bayanin ya zo ne don yayi Sallah.
Kimanin Falasɗinawa 7,326 ciki har da yawan ƙananan yara ne aka kashe sakamakon rikicin na yankin Gaza da Isra’ila, wanda aka fara tun 7 ga watan Oktoban da muke ciki.