Ƙasar Saudiyya ta tanadi kuɗi har Dala miliyan 13 don bayar da taimako ga fararen hula a Gaza, cibiyar samar da sassauci da jin ƙai ta sarki Salman ne su ka tabbatar da hakan a yau Alhamis.

Kuma sarki Salman na Saudiyya da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, su ne suka bayar da kuɗaɗen.
Cibiyar bayar da agajin da aka ƙirƙira a shekarar 2015, ta na aiki da ƙungiyoyin duniya kuma su na bayar da taimakon ga mabuƙata a ƙasashe kusan ɗari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, tun da yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Hamas, ofishin agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya ya buƙaci a samar da tallafi cikin gaggawa na kuɗi, kimanin Dala miliyan 300.
