Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori daya daga cikin kwamandojin ta, tare da binciken wasu mutane biyar bisa laifin kawo cikas a yaki da lalata da zamantakewa a jihar.

Shugaban hukumar Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ya ce an samu kwamandan da aka kora da aikata rashin da’a, yayin da ake ci gaba da binciken sauran wasu mutane biyar.
Ya bayyana cewa jami’in da aka kora ya saba hada kai da mugayen mutane don tafka munanan ayyuka a jihar.

Ya ce, sun kori Mataimakin Sufeto na Hisbah (DSH) tare da bayyana cewa ana neman sa, duk inda aka same shi a kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya.

A cewar sa ya kan hada kai da masu gudanar da otal din don kada hukumar Hisbah ta mamaye otal din nasu a yayin gudanar da ayyukanta.
Daurawa ya kuma musanta zargin cewa jami’anta sun aske gashin wani da ba dan asalin jihar ba da kwalba bayan sun kai farmaki gidan mata masu zaman kansu a jihar.
Wani mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook ne ya yi wannan zargin, amma Daurawa ya yi watsi da batun wanda ya alakanta a matsayin masu tada zaune tsaye.