Masu garkuwa da mutanen da suka yi garkuwa da dalibai biyar na jami’ar tarayya ta Dutsen-Ma da ke Jihar Katsina sun saki mutum daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa dasu.

 

A wata ganawa da BBC ta yi da shugaban jam’iar ya tabbatar da sakin daliba daya daga cikin ɗalibai biyar din da aka sace.

 

A yayin ganawar Shugaban bai bayyana cewa ko an biya kuɗi kafin sakin dalibar ba.

 

Shugaban ya ce za su yi duk iya bakin kokarinsu wajen ganin sauran mutane hudun sun kubta daga hannun ‘yan Ta’addan da suka yi garkuwa da su.

 

‘Yan Ta’addan sun sace daliban ne a ranar 4 ga watan Oktoba a dakunan kwanansu da ke cikin jami’ar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: