Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya Festus Keyamo ya bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da aiki a Najeriya ka-in da na-in nan ba da jimawa ba.

 

Keyamo ya ce jiragen za su dawo aikin ne bayan wata ganawa da yayi da wasu manyan masu ruwa da tsaki na Hadaddiyar Daular Larabawa.

 

Ministan ya kara da cewa a yayin ganawar sun yi magana da wakilan kamfanin na Emirates dangane da tashinsu daga Dubai zuwa Najeriya, tare da magance matsalolin da suka faru a baya.

 

Kazalika Keyamo ya ce gwamnatin Bola Tinubu na iyaka kokarinta kan sake dawo da jigilar jiragen.

 

Keyamo ya kuma bayyana cewa ya ziyarci manyan masana’antun sufurin jiragen sama a fadin duniya domin kulla alaka tsakaninsu da Najeriya.

 

Sannan ya ce da zarar kamfanin sun gama shirye-shirye za su sanar da ranar da za su fara aiki a Kasar.

 

Idan ba a manta ba dai a watan Oktoba shekarar 2022 da ta gabata kamafanin na Emirates ya dakatar da gudanar da harkokinsa a Najeriya, biyo bayan gaza biyansa wasu kudade da ya ke bin kasar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: