Ministan kudi a Najeriya Wale Edun ya ce, asusun gwamnatin tarayya na kara bunkasa sakamakon kudin shiga da ake cigaba da samu sanadiyar cire tallafin man fetur a kasar.

A cewar ministar, yanzu kudaden da ake samu ya haura tiriliyan daya, a tsawon watanni hudu da su ka gabata.

Ya bayyana haka ne, a ranar Litinin,  a garin Asaba na jihar Delta, yayin bude taro na kwanaki hudu don wayar da kan manyan akantoci masu lura da asusun gwamnatin tarayya.

Ministar wadda ya samu wakilcin sakataren dindindin na ma’aikatar Okokon Odu, ya ce gwamnati ta yi farar dabara na janye tallafin man fetur, domin ta lura cewa dogaro da man fetur ba abu ne da zai haifarwa yan Najeriya da mai ido ba.

Ya kara da cewa, yana daga cikin kudiri da manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, kyautatawa yan Nijeriya.
Don haka gwamnatin ta himmatu kwarai wajen ganin ta biya bukatun ya Najeriya tare da faranta musu

Leave a Reply

%d bloggers like this: