Fadar shugaban Kasa ta mayar da martani bisa kalaman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, dangane da gwamnoni ukun da Kotun daukaka ƙara ta tsige bayan shigar da kara gabanta.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai bai’wa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ba ya tsoma baki a harkokin bangaren shari’a, musamman ganin yadda mutane ke zargin shugaban na kokorin maida Kasar a tsarin jam’iyya daya.

Ya kara da cewa kalaman na Atiku na yinsu ne domin zafafa al’amuran siyasa da kuma tada hankula a Kasar baki daya.

Sanarwar ta kara da cewa ya kamata a’ummar Kasar su yi watsi da wadannan zarge-zarge na Atiku da ya ke yiwa jam’iyyar ta APC.
Daga karshe sanarwar ta yi kira ga jamiyyar PDP da Atiku da su guji furta kalaman da basu dace ba game da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke.