Gidauniyar Balarabe Goronyo da ke jihar Sokoto ta raba tallafin littafan karatu dubu uku a jiya Juma’a a jihar.

Ta kuma raba kayan makaranta guda 150, ga marayu da kuma ƴaƴan marassa gata da ke karatu a makarantun jihar.
Wakilin gidauniyar Junaidu Aliyu Balarabe, ya bayyana jin daɗinsu ga ƙoƙarin nasu na kyautatawa al’umma.

Ya ce ƙudurin gidauniyar shi ne taimaka marasa ƙarfi, don su samu damar samun ilimi a kowanne mataki don su amfani kansu da kuma al’umma nan gaba.

Junaidu ya ƙara da cewa bayan tallafawa ɓangaren ilimi, su na kuma bayar da taimako a ɓangaren lafiya ga marasa lafiya masu rauni a Sokoto da kewayenta.
Ya kuma buƙaci sauran masu arziki da rukunansu, da su yi koyi da su dan bunƙasar fannin ilimi a ƙasar nan.
An yi rabon kayan tallafin karatun ne dai ga marasa ƙarfi, a yankuna Ƙofar Bai, Galadanci, wasu yankunan Gidadawa da Ƙofar Rini a cikin birnin Sokoto.