Kakakin majalisar jihar Rivers, Edison Ehie ya wofantar da kujeru 25 na ‘yan majalisun da suka zabi yin biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike.

 

Kakakin majalisar ya bayyana hakan a zaman majalisar na safiyar yau Laraba, inda ya ce sashe na 109 (1) (g) da (2) na kundin dokar Najeriya ya ba shi ikon yin hakan.

 

Yan majalisu 25 da majalisar ta ayyana kujerunsu matsayin wofi, su ne suka sauya shekara daga PDP zuwa jam’iyyar APC a ranar Litinin.

 

Yan majalisar da ke biyayya ga Gwamna Siminalayi Fubara, sun yi zaman ne a fadar gwamnatin jihar da ke Fatakwal, inda gwamnan ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024.

 

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gwamna Fubara ya ba mambobin majalisar wani matsugunni a gidan gwamnatin don gudanar da zamansu.

 

A safiyar yau ne manema labarai suka ruwaito cewa an fara rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers biyo bayan wata gobara da ta kama wani shashe na majalisar a ranar 29 ga watan Oktoba.

 

Gwamna Siminalayi Fubara, ya isa majalsiar jihar Rivers don gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na jihar.

 

Gwamnan ya isa matsugunnin majalisar da ke a fadar gwamnatin jihar da misalin karfe 9 na safiya, wanda ya samu tarbar kakakin majalisar, Edison Ehie.

 

Fubara ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo, kwamishinan kudi, Isaac Kamalu, kwamishinan watsa labarai Joseph Johnson da wasu mukarrabansa.

 

Majalisar zartaswar jihar a zamanta na biyar a ranar Litinin, ta amince da Naira biliyan 800 matsayin kasafin kudin 2024 wanda su ke sa ran zai dawo da martabar jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: