Gwamnatin jihar Kano ta amince da ta biya diyyar Naira Biliyan uku ga ƴan kasuwar Masallaci Idi da ƙungiyoyin ƴan kasuwa da aka rushewa shaguna ba bisa ƙa’ida ba.

An cimma wannan yarjejeniyar ne dai ta cikin wani ƙorafin bisa sharuɗɗa da sasanci da aka shigar gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa amincewar wakilan ɓangarorin biyu ranar 13 Ga watan Disambar nan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa biyo bayan rushe shagunan bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, mutane 56 a madadin kungiyarsu sun shigar da ƙara mai lamba FHC/KN/CS/208/2023 a reshen kotun na Kano.

Masu ƙorafin sun shigar da ƙarar Gwamnatin jihar Kano, Hukumar tsara birane da cigaba, da kuma Kwamishinan shari’a na Kano.

Sai kuma hukumar ƴan sanda da suka yi ƙarar mataimakin babban sufeton ƴan sanda na rukuni na ɗaya, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, sai rundunar jami’an tsaro masu tsare fararen hula ta NSCDC reshen jihar Kano.

Mai shari’a Samuel Amobeda na babbar kotun tarayya a ranar 29 ga watan Satumba, ya umarci gwamnatin Kano Ta biya ƴan kasuwar diyyar Naira Biliyan 30 a maimakon Naira Biliyan 250 da suka nema akan rushe musu dukiyoyinsu ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: