Gwamnatin tarayya ta cire manyan makarantun gaba da sikandire a suka haɗar da Jami’o’i da kwalejojin fasaha daga tsarin biyan albashin bai ɗaya na IPPIS.

Gwamnatin ta ce daga yanzu makarantun za su dinga biyan albashin ma’aikatansu ne, ta hanyar tsarukansu da suke amfani da shi.

Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a zaman majalisar zartaswa a jiya Laraba a Abuja.

Ya kuma ce hakan wani ɓangare ne a ƙoƙarin da gwamnatin take yi, na rage ƙalubalen da ke fuskantar manyan makarantun gaba da sikandire.

Sannan kuma dai, makarantun a yanzu za su dinga ɗiban ma’aikatansu da kansu, ba tare da sa hannun daga ofishin shugaban ma’aikata na ƙasa ba.

Idan za a tuna, an sha takun saka tsakanin tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU akan wannan batu, tun a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: