A lokacin da ‘yan Najeriya ke kukan rashin wadatacciyar wuta, gwamnatin Tinubu na shirin fitar da Naira biliyan 600 don biyan kudin tallafin wutar lantarki na shekarar 2023.

Shugaban hukumar alkinta wutar lantarkin Najeriya Engr. Sanusi Garba ya sanar da hakan a wani taron tsare-tsaren samar da wutar lantarki da ya gudana a Abuja.

Garba ya ce gwamnatin ta yi kokarin rage kudin tallafin wutar lantarki daga Naira biliyan 528 zuwa Naira biliyan 144 a shekarar 2022, amma wannan shekarar, kudin sun karu.

Ya ce babbar matsalar da fannin wutar lantarki ke samu shi ne rashin biyan kudin wuta da ‘yan Najeriya ke yi, da rashin biyan harajin kamfanonin DisCo na kasar.

Ko a cikin watan Oktoba, sai da jaridar The Cable ta ruwaito gwamnati na cewa ta kashe Naira biliyan 171.25 wajen biyan tallafin wutar lantarki a watanni 6 na farkon shekarar 2023.

Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya ce akwai bukatar samar da wani kamfani daga kamfanin TCN da zai taimaka wajen bukasa rarraba wutar lantarki da samar da ita.

Adelabu ya ce rashin ingantattun kayan ayyuka a kamfanin TCN ya sa kamfanin ba ya iya samar da wutar da za ta ishi amfanin ‘yan Najeriya.

Ya kuma tabbatar da kokarin gwamnati na yin amfani da wasu hanyoyin samar da lantarki a kasar da suka hada da hasken rana, iska, da sauran makamashi don wadatar da wutar a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: