Aƙalla mutane biyu ne su ka rasa rayuwarsu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya faru a jihar Adamawa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Gamadio dake ƙaramar hukumar Numan ta jihar Adamawa.

Hatsarin ya afku bayan da kwale-kwalen ya kife da mutane biyar a yankin ciki har da wata uwa da yarta.

Da yake bayyana faruwar lamarin Mr Christopher Sofore shugaban ƙaramar hukumar Numan ya ce sauran mutane uku an riga an cetosu.

Sai dai har yanzu ba a gano gawarwakin ragowar mutum biyun ba.

Sofore yayi maganar ne a lokacin da tawagar gwamnatin jihar karkashin jagorancin mataimakiyar gwamnan jihar Kaletopwa George ta ziyar ƙaramar hukumar.

Farfesan ta yi ira da a samar da rigunan ruwa domin rage asarar rayuka.

Daga karshe ta gargadi mutane dasu tabbatar sun kai rahoton faruwar lamarin ga hukumomin da abinda ya shafa domin kare tseratar da rayuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: