An kama wasu ’yan sanda biyar da aka kama suna rakiya da ba da kariya ga dillalan miyagun kwayoyi wajen yin safarar hodar Iblis.

Dubun ’yan sandan da ake tsare a halin yanzu ta cika ne a lokacin da suke rakiyar dilar hodar Iblis mai tarin yawa da misalin karfe 3 na asuba a Jihar Legas.
Wadanda aka kama din suna aiki ne a runduna ta musamman na shugaban ’yan sanda kan yaki da muggan laifuka.

An kama su ne bayan musayar wuta da ’yan sandan farin kaya da suka samu labarin mugun aikin, suka kuma yi kokarin kama dillalan kwayoyin a yankin Victoria Island.

Wani babban dan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa bayan an tsayar da wadanda ake zargin domin bincike sun fara barazana ga jami’ansu suna harbi a iska.
Sai dai duk da haka, jami’ansu suka ki janyewa su bar su su wuce, da aka bincika kuma sai aka kama su da tulin miyagun kwayoyi wanda bayanai suka nuna hodar iblis ce.
Jami’in ya ci gaba da cewa, ana cikin haka sai jami’an NDLEA suka iso wurin, amma da suka nemi su tafi da kwayoyin sai wadancan suka ci gaba da harbe-harbe, suna neman hana su.
Wadanda aka kama a cewarsa, sun hada da wani mukamin DSP, Fayomi Abraham, ASP Emmanuel Bentong, Inspector Salami Femi, Inspector Ashimi Adedokun da Sajan Alex Akeredolu.
Wani mai mukamin mataimakin Kwamishinan ’yan sanda Ali Mohammed Ari ne ya kai su ofishin AIG Ali domin fuskanar bincike in ji jami’in.