Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda, ya mika takardun kama aikin din-din-din ga sabbin malamai 7,325 da aka dauka aiki a gwamnatin sa.

Gwamnan wanda ya taya malaman murna, ya bukaci su kasance masu yin aiki tukuru kasancewar koyarwa tamkar jihadi ne saboda Allah.
Ya ce Allah ne ya ba su wannan dama don yi wa al’umma hidima, don haka su kasance malamai masu aiki da tsoron Allah da kuma koyarwa bisa gaskiya.

Dikko Radda ya ce Allah ne ya zabe su, kar su ci amanarsa, su yi abin da ya dace kuma kar su ci amanar jihar su, ba zasu iya yi musu hisabi ba, amma Allah na jiran kowa a madakata.

Gwamnan ya kara da cewa ma’aikatar ilimi na samun sauye-sauye a jihar, don haka akwai bukatar sabbin malaman su zage damtse don bunkasa harkar ilimin jihar.
Gwamna Radda ya kuma yi alkawarin horas da sabbin malamai kafin tura su wuraren da za su yi aiki, inda ake sa ran za su kama aiki a ranar 6 ga watan Janairu, 2024.