Hukumar jami’ar tarayya da ke garin Dutsin-ma a jihar Katsina ta ce ragowar ɗalibanta mata huɗu da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci.

Mataimakin shugaban jami’ar (VC), Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi, shi ne ya tabbatar da haka yayin zantawa da ƴan jarida a Katsina ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.

Ya bayyana cewa ɗaliban guda huɗu da Allah ya sa suka tsira a yanzu, suna daga cikin ɗalibai biyar da ƴan bindiga suka sace kwanakin baya.

Idan ba ku manta ba, mahara sun yi awon gaba da ɗaliban ranar 3 ga watan Oktoba, 2023 a gidan da suke zaune na haya da ke bayan makarantar Mariyamu Ajiri memorial school a Dutsinma.

Shugaban jami’ar ya ƙara da bayanin cewa ɗaliban da suka kubuta a halin yanzu za a duba lafiyarsu a asibiti gabanin miƙa su ga danginsu.

Idan baku mantaba a baya Matashiya TV ta kawo muku rahoton yadda rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai mata 5 na jami’ar tarayya ta Dustinma a watan Oktoba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: