Gwamnatin tarayya a karkashin ma’aikatar aikin noma ta kasa ta tallafa wa manoman alkama a jihar Katsina.

Gwamnatin ta tallafa musu da ingantaccen irin alkama buhu biyu mai cin kilo hamsin hamsin da buhun taki 10 da maganin feshi na kashe ciyawa tare da takin zamani na ruwa wanda kundisu ya kai naira dubu 300,000.

Manoman za su biya kashi 50 bisa 100 na kudin kayan fa su ka karbar dubu wato 180,500 sannan take kafin su dauki kayan.

An raba manoman alkaman zuwa shiyyoyi bakwai a fadin jihar, a shiyyar Malumfashi ta kunshi kananan hukumomi 5, kananan hukumomin sune Kafur, Kankara, Bakori, Danja da karamar hukumar Malumfashi.

Inda manoma 653 za su amfana da shirin a shiyyar Malumfashi, kanfanin Agro Dealer shi ne kanfanin SHALTEN ne ya samar da ingantattun kayan.

Jagoran kanfanin Malam Ibrahim Muhammad wanda ake kira da Big G Funtuwa ya tabbatar wa manoman cewa, kanfanin su ya kawo ingantaccen iri da taki mai kyau da sauran kayayyaki.

Malam Ibrahim ya yaba wa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu wajen inganta noma a kasar nan, ya ce, shirin ya sha banban da sauran shirin da aka taba yi wajen bunkasa noma musamman noman alkama.

Ya ce gwamnatin tarayya da gaske take wajen kawo karshen tsadar matsalar abinci.

Wasu daga cikin manoman da suka fito daga kananan hukumomi Kafur, Malumfashi da Danda, Alhaji Garba da Hajiya Hadiza Muktar Malumfashi sun yaba wa gwamnatin tarayya wajen kawo wannan shirin na tallafa wa manoma don haka su ka yi kira ga gwamnati da ta cigaba da haka a nan gaba don magance matsalar tsadar kayan abinci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: