Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci jakadun kasashen waje da ke Najeriya da su ba da fifiko wajen binciko sabbin hanyoyin kasuwanci don ciyar da ƙasar gaba.

Shugaban ya kuma roƙe su da su yi amfani da waɗanan hanyoyin wajen faɗaɗa kasuwanci a tsawon lokacin da zasu kwashe na gudanar da ayyukansu.

Bola Tinubu ya yi wannan kalamai ne ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba, 2023 yayin da ya karɓi bakuncin sabbin jakadun da wasu ƙasashe suka turo Najeriya.

Kamar yadda manema labarai suka ruwaito, jakadun da suka gana da Tinubu sun haɗa da na ƙasar Hungary, Lorand Endreffy, jakadan Ruwanda, Christophe Bazivamo da na Ukraine, Ivan Kholostenko.

Shugaban Kasar ya kuma baiwa masu zuba jarin kasashen waje tabbacin cewa zasu samu kuɗin da suke tsammani da riba kuma za a daidaita tsarin haraji.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Juma’a.

Da yake jawabi yayin da ya karɓi bakuncin jakadan Ruwanda, Bola Tinubu ya ce kuɗaɗen da ake ta kace-nace da suka maƙale nan ba da jimawa ba za a sakar musu haƙƙinsu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: