Babban hafsan tsaro na kasa, Christopher Musa, ya sha alwashin cewa duk sojan da aka gano yana da laifi a kisan masu Maulidi a Kaduna zai ɗanɗana kuɗarsa.

A ranar 2 ga watan Disamba, jirgin yaƙin sojojin Najeriya mara matuƙi ya yi ruwan bama-bamai a taron bikin tunawa da haihuwar Manzon Allah SAW a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar.
Harin bama-baman, wanda rundunar soji ta ce kuskure ne, ya yi ajalin Musulmai sama da 100 a jihar Kaduna.

Tuni dai rundunar sojojin kasa suka ɗauki alhakin kai harin, tana mai cewa dakarun sojin na kan aikin yaƙi da ƴan ta’adda lokacin da suka jefa bam ɗin bisa kuskure.

Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Musa ya ce lamarin abin takaici ne matuka saboda aikin sojojin shi ne kare rayukan fararen hula.
Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasa ya jaddada cewa binciken da za a gudanar kan lamarin zai gudana a buɗe babu ƙunbiya-ƙunbiya.