Kotun kolin Najeriya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamban shekarar da muke ciki a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan Kano.

Daya daga cikin lauyoyin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf,ne ya tabbatar da ranar da za a yanke hukuncin na karshe ta cikin wata takardar da Kotun Kolin ta aike na sanar da ranar da za ta yanke hukuncin.

Gwamnan Jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ne dai ya shigar da kara gaban kotun ta Koli,ya na mai neman a yi masa adalci,akan kwace masa kujerarsa da kotun baya suka yi.

Shigar da karar da gwamnatin ta Kano ta yi na zuwa ne bayan da kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar ta kwace kujerarsa, tare da tabbatar da Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda shine ya samu nasara a zaben.

Hakan ne kuma ya sanya gwamnatin ta sake daukaka kara zuwa kotun daukaka kara,inda itama ta tabbatar da Gawuna a matsayin wanda ya samu nasara a zaben na 2023.

Bayan shigar da kara gaban kotun ta Koli da gwamnatin ta yi ne ta sanya ranar Alhamis din a matsayin ranar da za ta yanke hukunci akan karar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: