Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin jihar za ta sake nazari a kan dokar da ta kafa ƙarin masarautu a jihar.

Kwankwaso wanda ya bayyana a wata hira da yayi da kafofin watsa labarai daren ranar Alhamis a jihar.


Hirar na zuwa ne bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
Yayin da aka yi masa tambaya a kan ƙarin masarautu da gwamnatin da ta shude ta yi, Kwankwaso ya ce zuwa yanzu dai babu wani shiri da aka yi a kai, amma tabbas nan gaba kaɗan za a sake duba dokar.
Bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna Abba Kabir, magoya bayansu ke ta kirayen dawo da sarki Muhammadu Sanusi ll mai murabus.
Idan ba a manta ba, gwamnan Abba Kabir ya lashi takobin rushe dukkan wani tsari da aka yi musamman wanda bai yi daidai da tsarin tafiyar mulkinsa ba.