Wata kotu a jihar Jigawa ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mutane biyu.

 

Alkali justice Musa Ubale na babbar kotun jihar da ke zaune a Birnin Kudu ne ya karanto hukuncin.

 

An yankewa Habibu Haruna hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da aikata fyade.

 

Kotun ta karɓi kwararan shaidu guda biyar da su ka tabbatar da matashin ya ɗauki yarinya mai shekaru 14 ya kaita dakin matarsa ya rufe mata baki ya aikata laifin.

 

Sannan an yankewa wani Muhammad Musa Danzuga hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da aikata luwadi da wani mai shekaru 13 a duniya.

 

Alkalin mai shari’a Musa Ubaleya tabbatar da laifin da ake tuhumarsu da shi, daga bisani ya yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon rayuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: