A daidai lokacin da kae ci gaba da fuskantar karancin dalar Amurka darajar naira ta sake faduwa a kasuwar chanji.

Ko a jiya Alhamis ana chanjin dala ɗaya kan naira 1,355 a kasuwar bayan fage.
Rahotanni daga kasuwar chanjin a Abuja, Kano da wasu jihohin Najeriya sun nuna yadda ake samun ƙarancin dalar da kuma hauhawar farashinta.

Watanni biyar kenan ana samun faduwar darajar naira tun bayan da dalar ta koma sama da naira dubu ɗaya.

Hauhawar farashin ya ta’azzara ne bayan da gwamnatin ƙasar ta karyar da darajar naira a hukumance.
Karyar da darajar naira ya sa aka fara fuskantar ƙarin farashin man fetur, da sauran kayan amfanin yau da kullum musamman waɗanda ake shigo da su daga ƙasashen ketare.
Masana na hasashen cewa hauhawar farashin dala da karyewar darajar naira na iya sanyawa a sake samun ƙarin rufewar kanfanunuwa a Najeriya.