Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kutsa kai cikin rukunin gidajen sojoji sun sace mutane biyu a Abuja.

Al’amarin ya faru a jiya Alhamis da misalin ƙarfe 10:00pm na dare.
Yan bindigan sun shiga rukunin gidajen da ke Phase 2 a cikin rukunin gidajen.

Sai dai daga bisani jami’an tsaro sun mamaye rukunin gidajen bayan an yi awon gaba da mutane biyun.

Wani da lamarin ya faru yana yankin ya ce kwatsam su ka fara jin harbe-harbe cikin dare kuma a lokacin ne su ka tafi da mutanen.
Mutanen sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya mayar da hankali domin samar da cikakken tsaro.
Al’amarin tsaro dai na ce gaba da tabarbarewa a Najeriya musamman a yan makonnin nan.