Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta kara aike da karin jami’an tsaro zauren Majalisar dokokin Jihar bisa rikicin siyasa da ya ki ci ya ki cinyewa.

 

Rundunar ta kara aikewa da jam’an tsaron majalisar ne bayan ‘yan majalisar dokokin Jihar 16 na jam’iyyar PDP sun bayyana aniyyarsu ta komawa zauren Majalisar bayan kotun daukaka kara a Jihar ta koresu daga kan mukamansu.

 

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ta kara aikewa da karin jami’anne da misalin karfe 5:00 na Asubahin yau Talata a tsohon gidan gwamnatin Jihar.

 

Wani jami’in dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, an basu izinin bincikar dukkan wanda zai shiga domin gane ma’aikatan majalisar da kuma masu son tayar da rikici.

 

Rundunar ‘yan sandan Jihar ta Filato ta yi hakan ne domin dakile duk wani yunkurin masu son tayar da tarzoma a zauren Majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: