Gwamnatin Jihar Legas ta rufe wasu kasuwanni hudu a Jihar sakamakon karya dokar zubar da shara ba bisa ka’ida ba tare da rashin tsafta ce kasuwar.

 

A wata sanarwa da daaraktan kula da harkokin jama’a na hukumar kula da shara ta Jihar Misis Folashade Kadiri ta fitar.

 

Daraktar ta ce rufe kasuwar ya zama dole, domin kawo karshen matsalolin kiwon lafiya da Muhalli.

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kunle Adeshina ya fitar, ya ce kwamishinan Muhalli na Jihar Mista Tokunbo Wahab, ya ce gwamnatin Jihar ba za ta lamunci zubar da shara barkatai ba a Jihar.

 

Sanarwar ta ce hukumar kula da rashin Da’a da hukumar kula da shara ta Jihar, za ta dakatar da ayyukan wani kamfani mai yin robobi da mai raba robobin, bisa robobin na taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tsaftar muhalli a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: