Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawar da cin hanci da rashawa da sauran munanan dabi’u a fadin Kasar.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a yayin wata ziyara da kungiyar kiristoci ta ƙasa CAN ta kai masa fadar sa da ke Abuja.

 

Shugaban ya bukaci kungiyar ta CAN da ta fara gudanar da wa’azi akan gujewa cin hanci da rasawa da sauran ayyuka masu alaka da haka.

 

Shugaban ya kara da cewa yin hakan zai taimaka matuka wajen ganin an kawo matsalar da ta addabi Kasar.

 

Kazalika ya ce gwamnatinsa za ta hada hannu da ‘yan kasar wajen ganin an kawo karshen munanan dabi’u da su ka addabeta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: