Yan bindiga sun hallaka wasu fitattun sarakai guda biyu a karamar hukumar Ikole da ke jihar Ekiti.

 

Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da sarakan ke dawo daga wata ganawa ta tsaro a kauyen Irele-Ekiti.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda aka kashen sun hada da Elesun na Esun-Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsakin da Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olushola.

 

Yayin da Alara na Ara-Ekiti, Oba Adebayo Fatoba ya tsira da kyar daga mugun nufin ‘yan bindigan da suka yi kokarin yin ajalinsa shi ma.

 

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun so sace dukkan sarakunan ne guda uku a kan hanyar Oke-ako.

 

Shugaban karamar hukumar Ajoni, Michael Ogungbemi ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jaridu, kamar yadda Leadership ta tattaro.

 

Ogungbemi ya yi Allah wadai da kisan manyan sarakunan inda ya ce jami’an tsaro sun bazama cikin daji neman maharan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: