Wata majiya dake yawo an bayyana cewa za a tsige shugaban jamiyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje a nada Yahaya Bello.

Kamar yadda aka ga wasu fastoci suna yawo a babban birnin tarayya Abuja suna nuna cewa za a nada sabon shugaban jam’iyar kuma yahaya Bello zai gaje ta.


Majiyar dake yawo an bayyana cewa za a tsige shugaban jamiyar APC na rikon kwarya a nada Tsohon gwamnan jihar Kogi da ke zawarcin kujerar.
An jiyo wasu majiyoyi suna cewa ana so ne a karbe shugabancin jamiyar APC daga gurin Ganduje zuwa wurin Bello.
Sai dai tun a jiya aka hangi takardun hotunan yahaya Bello suna yawo tare nuna sha’awarsa ta neman hakan.
Kuma hakan yasa ake ganin Ganduje zai Kara da yahaya Bello wajen Neman kujerar.
Ganduje Wanda aka zaba a ranar biyu ga watan Augusta shi ma yana cikin wadanda su ke zawarcin kujerar.