Babbar kotun tarayyar Najeriya wadda aka fi Sani da kotun koli ta tabbatarwa da Ahmad Fintiri nasara a matsayin gwamnan jihar Adamawa a zaman da aka yi.

Kotun ƙoli a yau laraba ta kammala sauraron karar da aka shigar gabanta wadda jamiyar APC da Aisha Dahiru Binani suka shigar suna mai ƙalubalantar nasarar da Fintiri ya samu a zaben 2023.


Sai dai alkalin kotun Mai suna John Okoro ya bayyana cewa tabbas Gwamna Ahmad Fintiri ne lashe zaben da aka gudanar.
Okoro ya ci gaba da cewa tun farko ma ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zabe sabawa doka ne.
Kuma babu wanda zai yi hakan sai baturen zabe Kuma duk wanda yayi haka ya sabawa doka.
Sai dai alkalin ya ce Aisha Dahiru Binani ta kasa tabbatarwa da kotun cewa su su ka yi nasara don haka ya tabbatar da Fintiri a matsayin halattaccen Gwamna.
