Kotun dake sauraron shariar Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ta bayar da belinsa bayan gindaya wasu sharuda.
A zaman kotun na yau Alhamis alkalin kotun ya bayar da belin Dan Bilki Kwamanda.
Ya ce kafin ya bayar da belin amma sai an bi wasu sharudda kamar hakimi ya tsayawa Dan Bilki sannan da sakatare daga ma’aikatar gwammnati.
Sannan alkalin ya kara da cewa sai an ajiya naira miliyan daya kafin cin moriyar belin.
Da yake magana lauyan dan Bilki Barista Chedi ya bayyana cewa sun bi dukkan ka’idoji kuma kotu ta bayar da belinsa.
Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya dade ana fafata lamarin siyasa kasa musammama jihar kano.
Sai dai kotun na zarginsa da wasu kalaman tayar da tarzoma, sai dai kafin haka sai da ya shafe wasu kwanaki a gidan gyaran hali.



