Majalisar dattawan Najeriya ta shiga wata ganawar sirri da manyan shugabannin tsaron ƙasar yau.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya nemi afuwar ƴan majalisar bisa zaman ganawar sirrin da su ka shiga.


Daga cikin waɗanda su ka halarci zaman akwai babban hafsan tsaron ƙasa, da shugabannin sojon sama da na ƙasa da na ruwa.
Haka kuma akwai shugaban ƴan sandan Najeriya da babban mai bayar da shawara kan sha’anin tsaron ƙasa sai babba da ƙaramin ministan tsaron Najeriya.
Majalisar ta ɗauki matakin ganawar siriin ne bayan da ta samu korafe-korafe masu yawa kan sha’anin tsaro a Najeriya.
Har kawo wannan lokaci ba su bayyana matsayar da su ka cimma a kai ba.
A zaman majalisar na yau shugaban majalisar Godswill Akpabio ya rantsar da sabbin ƴan majalisar uku da aka zaba.
