Ƙungiyar masu dakon mai ta Najeriya NARTO ta shirya tsaf don dakatar da ayyukanta daga Litinin mai zuwa.

 

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Alhaji Lawal Othman ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

 

Ya ce kafin ɗaukar matakin sai da su ka aike da takarda ga sakataren gwamnatin tarayya, shugaban hukumar DSS, kamfanin mai na ƙasa, ma’aikatar mai ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Ya ce bayan aike da takarda a kan halin da su ke ciki, babu wanda ya basu amsa, aka yi halin ko in kula da buƙatunsu.

 

Ya ce farashin dakon mai da ake yi tun lokacin mulkin shugaba Muhammadu Buhari shi ake biyansu a wannan lokaci duk da cewar farashin dala ya ninka.

 

Ya ƙara da cewa a farashin da su ke yin aikin babu wata riba da su ke samu face faduwa.

 

A sakamakon haka su ka yanke dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin duk daa cewar tuni wasu daga cikinsu su ka fara ajiye motocinsu.

 

Ya ce idan mutum na da tankar mai ɗaya da ke ɗaukar lita 40,000 ya na asarar naira 114,000 a kowanne dako ɗaya.

 

A sakamakon haka su ka yanke shawarar dakatar da ayyukansu baki ɗaya daga ranar Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: