Gwaamnatin jihar Borno ta yi umarni ga mutane a jihar da su tashi da azumi da nufin neman sauƙi daga tsadar kayan masarufi.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya yi wannan kira yau Juma’a.


Ya umarci mutanen jihar da su tashi da azumi aa ranar Litinin bisa tsadar kayan masarufi da kuma barazanar tsaro a wasu manyan titunan jihar.
Ya ce ya damu bisa halin da ake ciki na tsadar rayuwa wanda ƴan jihar ke fama.
Zulum ta tabbatar da cewar gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa wajen farfaɗo da harkokin noma tare da haɓaka yawan noman da ake yi don magance matsalar.
Sannna gwamnatin jihar za ta aa hannu a harkokin noman zamani tare da tallafawa kananan manoma da kuma bunƙasa harkokin noma.
Gwamna Zulum ya nuna takaiaci a hisa wasu hare-hare da kae samu a manyan titunan jihar.
Za a tashi da azumin ne a ranar Litinin 19/2/2024.
