Majalisar wakilai ta tarayya ta tsallakke karatu na biyu a kan batun ƙirƙirar ƴan sandan jihohi.

Ƴan majalisa 13 ne su ka miƙa ƙudirin a zauren majalisar kuma su ka samu goyon bayan mafi rinjaye.


Za a samar da ƴan sandan jihohin ne domin taimakawa bangaren tsaro da matsalar taa ƙi ci ta ƙi cinyewa a Najeriya.
A makon jiya shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar inda su ka nuna sha’awar haka.
Daga cikin dalilai da su ka sanya aka nemi ƙirƙirar ƴan sandan jihohi akwai garkuwa da mutane, hare-hare a yankunan arewa da kudancin kasar.
Tun a baya wasu daga cikin gwamnoni su ka nuna aniyar haka, sai dai ba su samu dama ba a wancen lokaci.
Dalili ke nan da ya sa wasu jihohin kamar Borno, Katsina, Zamfara da Sokoto su ka kirkiri ƴan sa kai, domin magance matsalolin jihohinsu.
Zuwa yanzu ƙudirin ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar kuma bayan tsallake karatu na uku zai zama doka da zaa ta bai wa gwamnoni samar da ƴan sandansu.
