Rundunar sojin Najeriya ta yi gargadi ga ƴan ƙasar da ke kiraye-kiraye don yin juyin mulki.

Babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ne ya yi gargadin yayin da yake mayar da martani dangane da masu kira ga sojin don ganin sun karɓe ikon mulkin ƙasar.


Musa wanda ya yi bayanin yau bayan buɗe wani aiki a helkwatar rundunar sojin ta shida da ke Fatakwal a jihar Rivers.
Ya ce bai dace a dinga kira don ganin sun yi juyin mulki ba ganin yadda ake samun cigaba mai yawan gaske cikin kankanin lokaci a ƙarƙashin mulkin demokradiyya.
Ya ce abinda ya kyautu ga ƴan ƙasar shi ne su yi haƙuri don ganin sun ci ribar gwamnatin da ke mulkarsu.
Amma duk wanda ke kira da a yi juyin mulki to ba mai ƙaunar Najeriya ba ne kamar yadda ya shaida.