Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 84 a ƙasar cikin makonni bakwai.

Mutanen da cutar ta hallaka na a jihohi 23 na ƙasar.


Dakta Jide Idris da ke zaman babban darakta a hukumar shi ya bayyana haka yau yayin taron manema labarai.
Ya ce an samu tabbacin cutar ta kama mutane 476 yayin da ake zargi ta harbi mutane 2,621 a ƙananan hukumomi 84 na faɗin ƙasar.
Rahoton da aka tattara a ranar 18 ga watan Fabrairu da mu ke ciki.
Ya ce hukumarsu ta samu rahoton mace mace da aka samu a asibitin asibitin sojoji da ke Kaduna.
Kuma su na aiki da hukumar lafiya ta Kaduna domin gano dalilin barkewar cutar da ke hallaka mutane.
Kuma sun ɗauki samfurin jini mna mutane huɗu tare da aikewa da shi asibitin koyarwa da ke Kano don gudanar da bincike.