Shugaban Kasa Bola Tinubu ya je Jihar Ondo domin yin ta’aziyyar tsohon gwamnan Jihar Retimi Akeredolu bisa rasuwarsa.

Tinubu ya kai ziyarar ne ga iyalan gwamnan da ke garin Owo a Jihar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, baya ga ta’aziyyar shugaban zai kuma kai ziyarar girmamawa ga sarkin Owo Aba Ajibade Ogunoye.

Sannan zai kuma sake kaiwa jagoran kungiyar Al’adun Yarabawa ta Afenifere Cif Reuben Fasoranti.

Shugaban ya kai ziyarar ne bisa rakiyar gwamnan Jihar Lucky Aiyedatiwa da kuma wasu daga cikin shugabanni APC na Kasa da na Jihar.
Akeredolu ya mutu ne tun a watan Disamban shekarar 2023 da ta gabata bayan fama da rashin Lafiya inda aka binne shi a ranar Juma’ar da ta gabata a Jihar ta Ondo.