Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya aikewa da majalisar Jihar sunayen shuwagabannin riko na kananan hukumomin Jihar domin tantancewa.

Mai magana da yawun Majalisar Hon Ismail Falgore ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karanto takardar bukatar a yayin zaman majalisar da aka gudanar a jiya Talata.

Bayan kammala zaman majalisar shugaban masu rinjaye na majalisar Hussaini Dala ya yiwa manema labarai karin haske akan lamarin.

Husain ya ce sunayen da gwamnan ya aikewa majalisar sun kunshi mutane 17 da suka hada da shugaba mataimakin shugaban karamar hukuma, da sakatare a kowace karamar hukuma 44 na Jihar.

Dan majalisar ya bayyana cewa Majalisar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi da zai yi aikin tantance wadanda aka nada a yau Laraba.

Hussain kuma ya bayyana cewa za a yi nadin ne karkashin sashe na 58 (A) na dokar kananan hukumomi, bayan karewar wa’adin majalisar kananan hukumomi inda za a gudanar da zabe bayan kammala tantance mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: