Majalisar dokokin jihar Jigawa ta tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mai Tsawatarwa na Majalisar Dokokin Jihar.

Majalisar ta kuma dakatar da shugabannin kananan hukummi hudu, bayan karbar rahoton kwamitocin da ta kafa.


An tsige jagororin majalisar ne bayan samun su da laifin kitsawa da kuma goyon bayan yunkurin tsige shugaban majalisar a makonnnin da suka gabata.
Dan majalisa mai wakiltar Malam Madori, Hamza Ibrahim Adamu, ne ya gabatar da kudurin, wanda ya samu amincewar takwarorinsa.
Nan take bayan tsige Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Aliyu Ahmed, mai wakiltar Kirikasamma da kuma Mai Tsawatarwa, Dayyabu Shehu Kwalo, mai wakiltar Taura, majalisar ta maye gurbinsu.
Mambobin majalisar sun kuma dakatar da shugabannin kananan hukumomin Auyo, Dutse, Gumel, da Ringim, kan zargin badakalar kudade.
Majalisar ta ce dakatar da shugabannin kananan hukumomin alama ce na shirinta na bin diddigin kudade da kuma yin komai a fili a matakin gwamnatin jiha da kananan hukumomi.
