Rundunar ‘yan sanda a Legas ta tsaurara tsaro a ma’ajiyar abinci ta gwamnati da kuma manyan kantuna saboda gudun kai hari na bata gari.

 

Rundunar ta dauki matakin ne yayin da wasu jihohi ke fuskantar barazanar fasa wuraren ajiyar abinci yayin da ake cikin wani hali.

 

Har ila yau, Hukumar ba da agaji ta NEMA ta tsaurara tsaro a wuraren da take ajiyar kayan abinci a yankin.

 

Kwamishinar ‘yan sanda a jihar Legas, Adegoke Fayoade ta ce sun baza jami’an ‘yan sanda masu farin kaya don kula da wuraren.

 

Fayoade ta umarci dukkan turawan ƴan sanda da ke jihar su zauna cikin shirin ko ta kwana domin dakile faruwar harin a fadin jihar baki daya, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya bayyana haka ga manema labarai ta wayar tarho.

Leave a Reply

%d bloggers like this: