Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bukaci a biya ma’aikatan jihar Akwa Ibom N850,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Sunny James ne ya bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a da gwamnatin tarayya ta shirya kan mafi karancin albashi a garin Uyo, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
Mista James ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda har yanzu wasu jihohin yankin ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 wanda aka sake nazari a shekarar 2019.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, James ya ce ya kamata a sauke duk gwamnan da ya ki biyan N850,000 a gidan yari.

Duk gwamnan jihar da ya ki biyan sabon mafi karancin albashi toh a daure shi.
Sakataren kungiyar na jihar, Kwamrad Kinsley Bassey ya ce gwamnatin Najeriya na biyan ma’aikata albashin mafi ƙanƙanta.
Ya ce a matsayinsu na ma’aikatan Najeriya, suna samun albashin bauta ne idan aka yi la’akari da tsadar rayuwa.
